Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
A kokarin Gwamnatin Muhammadu Buhari na ganin an kawo karshen shigowa da makamai cikin tarayyar Nijeriya shugaban tare da shugaban hukumar yaki da masu fasa kwauri Hameed Ali za su kai ziyara kasar Turkiyya.
Kamar yadda mataimakin shugaban rundunar kwastan ta Nijeriya ya fitar da sanarwar cewa an shirya wannan kai ziyara ne kasar Turkiyya domin tattaunawa a kuma duba irin yadda ake ta samun matsalar shigowa da makamai cikin Nijeriya daga kasar Turkiyya.
In dai za a iya tunawa a kwanan baya ne aka samu matsalar shigar da makamai musamman sababbin bindigogi cikin Nijeriya duk daga Turkiyya wanda ake ganin ya saba wa ka\’ida da kuma tsarin zaman tare da ake dangantaka tsakanin kasa da kasa.