An Kashe Mutum 35 A Jihar Filato

0
798

Rabo Haladu Daga Kaduna

AKALLA mutum 35 aka kashe yayin da aka jikkata wasu da dama a hare-haren da aka kai wasu
kauyuka a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
Wasu \’yan bingida ne dai suka kai hare-haren a ranakun Lahadi da kuma Litinin, inda suka lalata
gidaje da dama.
Rahotanni sun ce hukumomi sun sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin inda aka tura karin jami\’an tsaro.
A halin yanzu manyan jami\’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a jihar Filato suna tattauna yadda za a kawo karshen tashe tashen hankula.
Mutane da dama ne suka mutu a \’yan shekaru baya a tashe-tashen hankula masu nasaba da
kabilanci da addini a jihar.
Sai dai a \’yan watannin baya, an samu kwanciyar hankali a jihar bayan yarjejeniyar zaman lafiya da
aka cimma da bangarorin da ke rikici da juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here