Macizai Na Sarar Fiye Da Mutum Miliyan Biyar Duk Shekara – WHO

0
747

Rabo Haladu Daga Kaduna

MUTANE kimanin miliyan biyar da dubu dari hudu ne dai maciji kan sara a duk shekara a duniya,
adadin wadanda kan rasa rayukansu kuma ya kama daga 91,000 zuwa 130,000 kan rasa rayukansu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) ta bayyana.
Akwai kuma mutane da dama da ke rasa gabbansu da kuma nakasa sanadiyyar saran macijizai.  dai na daya daga cikin da macijin ke barna sosai. Wakilinmu Rabo Haladu ya ziyarci yankin Kaltungo da ke jihar
Gombe, daya daga cikin wuraren da matsalar ta fi kamari a Najeriya.
Al\’umomi da dama a kasa dai na rayuwa ne kullum cikin fargaba saboda da matsalar sarar majici, musamman yanzu da damina zuwa kaka.
Manoma da kuma kananan yara ne matsalar ta fi shafa. Da dama daga cikinsu akan kai su asibitin jinyar
sarar maciji ne da ke garin Kaltungo, daya daga cikin cibiyoyi kalilan na musamman domin jinyar
sarar maciji .
An kawo wata yarinya mai suna Haraja, mai shekaru goma sha shida wannan asibiti a sume, kwana hudu bayan da maciji ya sare ta.
Cikin kasa da sa\’o\’i ashirin da hudu daga bisani kuma budurwar ta rasu. Daga nan ne sai aka yi jana\’izarta a wata makabarta da ke kusa da asibitin ya sanya jinkiri kai ta cibiyar ta sarar maciji.
Kububuwa ce ta fi kai wa mutanen wannan yankin farmaki, inda take sararsu ba babba, ba yaro.
Wata dattijuwa mai suna Misis Trihana Yayinus, wadda take kwance a gadon   asibiti ta ce ta sha azaba a wajen kububuwa domin kwananta uku a sume bayan ta  sare ta a gona.
Wata babbar matsalar dai ita ce yadda wadanda macijin kan sara ba sa samun magani yadda ya kamata.
Ba a yin maganin a Najeriya amma akan shigo da maganin ne daga kasar Birtaniya da kuma yankin
kudancin Amurka bayan an kai samfurin macizan da kuma dafin daga Najeriya.
Wasu lokuta dai magani kan kare karkaf a cibiyar ta Kaltungo, amma a kullum marasa lafiya sai kwarara suke yi domin neman maganin.
Ko baya ga wadannan alkaluma, akwai kuma wasu dubban a wasu yankuna na Najeriya wadanda macijin kan sara a duk shekara.
Kuma masana na cewa samar da magani a kan kari da kuma kai duk wanda maciji ya sara asibiti da wuri za su taimaka matuka wajen rage yawan mace-macen.
Hakan kuma zai kawo karshen wahalar da daya daga cikin halittu mafiya hadari a duniya ke
haddasawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here