Rabo Haladu Daga Kaduna
A garin Sarkin Pawa, hedkwatar karamar hukumar Muya a jihar Neja, wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da babban jami’in ‘yan sandan yankin tare da dogarinsa kuma har yanzu babu labarin inda suke wasu ‘yan bindiga sun jefa al’ummar garin Sarkin Pawa, hedkwatar karamar hukumar Muya, cikin zaman zullumi sanadiyar sace babban jami’in ‘yan sandan yankin tare da dogarinsa.
Shugaban karamar hukumar Muya, Yahuza Muhammad Kuti, ya ce baicin babban jami’in ‘yan sandan da
dogarinsa da ‘yan bindigan suka sace akwai kuma wasu mutane hudu da su ma an sace su, kamar yadda ya yi wa manema labarai bayani.
Wasu mazauna garin sun tabbatar da aukuwar lamarin da yammacin jiya.
Gwamnatin jihar ta Neja ta ce ta damu da aukuwar lamarin, a cewar Kanar M.K. Maikundi, wani hadimin
Gwamnan jihar na mausamman a kan harkokin tsaro.
Sai dai kuma Kwamishanan ‘yan sandan jihar ta Neja ya ki ya ce komai