Za A Sallami ‘Yan Boko Haram 468 Masu Fuskantar Shari’a

0
674

Rabo Haladu Daga Kaduna

OFISHIN ministan shari’ar  ya sanar da sallamar wasu ‘yan Boko Haram su 468 cikin wadanda ake tuhuma saboda bincike ya nuna basu aikata wani laifi ba, kazalika za’a saki wasu da ba’a sami wata kwakwaran shaida a kansu ba, kodayake ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro zai yi musu horon
sake hali
Ofishin ministan shari’ar  kuma Antoni Janar ya bada sanarwar sakin mutane 468 saboda ba a same su da wani laifi ba. Su dai wadannan mutanen za’a mika su ga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Sai dai kawo yanzu kotun ta yanke wa mayakan ‘yan Boko Haram 45 hukuncin daurin shekaru bisa ga
laifukan da suka aikata. Wasu 116 suna fuskantar karin tuhuma yayin da aka ce babu isasassun shaidu a kan wasu 334.
Wani rahoto da babban mai gabatar da kara da sunan gwamnatin Najeriya, Muhammad Umar Yusuf ya gabatar ne ya tabattarda cewa wasu ‘yan Boko-Haram da ake tuhuma suna fuskantar shari’a a babbar kotun tarayya da ke Bauci. Akwai wasu 28 da za a maida shari’arsu a manyan kotunan tarayya a Abuja da Minna
Kawo yanzu dai an saurari kararraki 149 a kotuna hudu inda aka yi watsi da shara’oi 34 sanadiyar rashin isassun shedu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here