An Sace Turawa \’Yan Mishan A Nijeriya

0
850

Rabo Haladu Daga Kaduna

AN yi garkuwa da wasu mutum hudu da ake zargin \’yan kasar Biritaniya ne a jihar Delta
Kakakin ofishin \’yan sandan jihar Andrew Aniamaka, ya ce mutanen \’yan mishan ne da ke
zama a wani kauye a yankin, inda suke ayyukan bayar da kiwon lafiya kyauta.
Cikin wadanda aka sace din har da wasu ma\’aurata, inda da misalin karfe 2:00 na daren
ranar Juma\’a ne wasu \’yan bindiga suka dirar musu.
Mista Aniamaka ya ce ya zuwa yanzu dai kungiyar da ke kiran kanta Karowei wadda ake
zargin ta da sace mutanen, ba ta bukaci kudin fansa ba tukunna.
Basarken kauyen ya shaida wa manema labarai  cewa \’yan mishan din likitoci ne da suka kwashe shekara
goma suna zama a kauyen.
Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa dai ya zamo ruwan dare a yankin na Naija-Delta
mai albarkatun man fetur, kuma \’yan sanda na zargin akwai yiwuwar lamarin wani martani ne
dangane da yakin da ake yi da ta\’addanci a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here