Rabo Haladu Kaduna
GWAMNATIN Jihar Taraba ta musanta cewa ta lakume kudaden tallafi na Naira Miliyan 50 da hamshakin dan kasuwan nan Aliko Dangote ya ba da domin a tallafa wa wadanda rikicin yankin Mambila ya shafa
Wannan ne dai karon farko da Gwamnan Jihar Taraban, Arch.Darius Dickson Isiyaku ke maida martani game da bacewar Naira Miliyan hamsin da dan kasuwan Aliko Dangote ya ba da a matsayin gudummawa ga wadanda rikicin Mambilla ya shafa.
Ko a makon jiya sai da wasu shugabanin al’umman yankin Mambillan suka yi korafi na cewa fiye da watanni uku da bada gudummawar, har yanzu su ba su ga koda kwandala ba.
To sai dai a martanin da ya maida, Gwamnan jihar, ta bakin mataimakinsa Haruna Manu, ya ce kawo alkawari kawai Dangote ya yi, domin babu ko anini da ya shigo aljihunsu,balle a raba.
To ko ya lamura suke yanzu a yankin? Barrister Bashir Muhammad Bape, dan majalisar dokokin jihar Taraba da ke wakiltar mazabar Nguroje, ya bayyana cewa duk da hankula sun kwanta akwai
bukatar kai tallafi.
Jihar Taraba jiha ta fuskanci rikice-rikice da sau tari ke da nasaba da kabilanci ko addini, lamarin da ya
maida wasu yankuna kufai, inda wasu ma ke ganin akwai sakaci a lamarin.
Ambassada,Hassan Jika Ardo, wanda shi ne Jakadan Najeriya na yankin Caribbean na ganin akwai abin
dubawa a lamarin.