Matan Gwamnonin Arewa Sun Gudanar Da Taronsu A Bauci

0
789

Rabo Haladu Daga Kaduna

A taron nasu, matan gwamnonin arewa sun cimma matsaya kan wasu muhimman abubuwa da suka hada da matsalar shan miyagun kwayoyi da ilmin ‘ya mace tare da alkawarin mara wa mazajensu baya
Matan gwamnonin arewa sun yi taronsu na biyar a garin Bauci inda matar Gwamnan Bauci, Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar, ta zama shugabar kungiyar.
Taron ya tattauna kan wasu abubuwa da ke da mahimmanci. Wadannan ko sun hada da batun shawo kan matsalar shan miyagun kwayoyi, ilmin ‘ya’ya mata, goyon bayan shirin matar shugaban kasa da mara wa mazajensu baya domin su yi nasara a ayyukansu.
A jawabinta, sabuwar shugabar kungiyar Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar, ta jaddada goyon bayansu ga duka shirye-shiryen da za su kawo ci gaba, musamman ma ga mata.
Ita ma matar Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Adama Ibrahim Dankwambo, ta yi karin haske a kan muhimman abubuwan da suka tsayar a taron, inda ta nuna cewa kowa ya san illar da miyagun kwayoyi ke yi wa matasa da matan aure.
A sakonsa ga taron Gwamnan Bauci Muhammad Abdullahi Abubakar ya bukaci ganin matan sun bai wa
mazajensu goyon baya bisa ga duk ayyukan da za su yi nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here