Yunkurin Jihar Kaduna Na Ciwo Bashin Naira Biliyan 122 Ya Haddasa Yamutsi

0
627

Rabo Haladu Daga Kaduna

JIHAR Kaduna na cikin jihohin da suke neman ciwo bashi amma wannan lamarin ya rarraba kawunan ‘yan jihar inda har mata suka fito suna zanga zanga tare da dora wa Sanata Shehu Sani laifin kawo cikas ga yunkurin gwamnatin jihar Kaduna na ciwo bashi domin gudanar da wasu ayyuka na ci gaba da rarraba kawunan ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar.
Wasu mata da suka dorawa Senator Shehu Sani alhakin jawo jinkirin ciyo bashin sun fito sun yi zanga zanga a garin Kaduna,
Daya daga cikin matan da suka yi zanga-zangar, Hajiya Saratu Abdulaziz, ta yi wa manema labaru karin bayani, inda ta ce Sanata Shehu Sani ya yi masu alkawarin daukaka daraja martabar mata kuma shi ne shugaban kwamitin da ke da hakin amincewa da cin bashin amma ya ki sawa jiharsa hannu saboda wani dalilin da ke zuciyarsa.
Amma Kwamred Suleiman Ahmed da ke taimaka wa Sanata Shehu Sani a kan harkokin siyasa, yana ganin
wadanda ke zanga-zangar ba su binciki gano ko jihar Kaduna ce kadai ba’a ba bashin ba. Ya ce akwai jihohi akalla goma da ba’a ba su bashin ba. Ya kuma zargi masu zanga-zangar da tallata wani mutum daban da suke cewa shi ya cancanta ya zama Sanata din yankin. Ya ce har kudi aka dinga rabawa a wurin zanga-zangar tare da yawo da kwalaye da ke dauke da sunan wannan mutumen.
Yunkurin ciwo bashin ya sa wadanda suka raba gari da Gwamna Nasiru El- Rufai na jihar a jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna su soki lamirinsa. A cewarsu babu wani dalilin ciwo bashin.
Sun yi nuni de cewa a cikin shekaru 50 gwamnoni 19 da suka yi mulki a jihar sun ciwo bashin Naira Biliyan 80 ne kawai, yayin da gwamnatin yanzu ke neman ci wa Jihar Kaduna bashin da ya kai Dalar Amurka 350m, kwatankwacin Naira Biliyan 122.
Sai dai Malam Muhammad Namadi dan majalisar wakilai daga jihar yana goyon bayan a ciwo bashin saboda za’a yi wa al’ummar Kaduna aiki da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here