Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Taimaka Wa Tsofaffi A Wani Shirin Gwaji

0
666

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Sakkwato ta kaddamar da wani shirin taimaka wa tsofaffi marasa galihu da basu da mataimaka da suka hada da maza su dari biyar daga sassa daban-daban na Jihar Sakkwato don
saukake musu wahalhalun rayuwa da suke fama da su a cewar shugaban wannan shiri na jarrabawa Malam Lawal Maidoki sakamakon shirin ne zai bada tabbacin makomar shirin a fadin jihar baki daya. Kuma ya ce hukuma tana sa ran wannan taimako zai rage tsananin talauci da tsofaffi ke fama da su.
Taimakon zai hada da ciyarwa da tufatarwa da kuma kiwon lafiya musamman cututtukar da tsofaffin ke fama da su na yawan shekaru.
Gwamnatin jihar ta ce kowane tsoho ya taba taka wata muhimmiyar rawa a ci gaban jihar don haka ya kamata a kula da rayuwarsu ko da kuwa ba su haifu ba.
Wannan shirin gwaji da karkashin hukumar zakka da wakafi na Jihar Sakkwato zai kyautata rayuwar
tsofaffin da ba su da mataimaka, kamar yadda wadansu da suka ci gajiyar wannan shirin suka bayyana, sun nuna farin cikinsu ainun tare da mika dubun godiya ga gwamnati da ta yi wannan tunani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here