Ta Karyata Jita-Jitar Allurar Riga-kafi

0
767
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
A Kwanakin baya ne dai aka rika yada jita-jita a cikin garin Damaturu
da ma wasu sassan Jihar Yobe kan cewar wai an samu wasu mutane da ke
zuwa cikin wasu makarantun firamare da na gaba da Firamare da zimmar
yi wa yara allurar rigakafi maza a tsakar ka  mata kuma kasan cibiya
lamarin da ya haifar da tunziri daga iyayen yara da kuma malaman
makaranta.
Akan haka ne gwamnatin Jihar Yobe ba ta yi kasa a gwiwa ba yadda nan da
nan kwamishina ma\’aikatar kiwon lafiyar jihar Dokta Muhammad Bello Kawuwa
ya kira taron \’yan jaridu ciki har da GTK yadda ya karyata
wannan jita-jita tare da cewar wannan labari tamfar kururuwar shaidan
ne. Shin ma yaya za a ce wai za a yi allura a ka da kuma kasan cibiya?
Don haka ne kwamishinan ya kirayi jama\’a da su yi watsi da irin
maganganu marasa tushe balle makama domin farfaganda ne kawai daga
wasu bata-gari marasa son zaman lafiya a jihar. Kuma ma\’aikatarsa a
shirye take da ci gaba da fadakar da jama\’a a kan dukan
aikace-aikacenta ta kafofin yada labarai yin haka zai taimaka nan gaba
wajen kawar da irin wannan mummunan yanayi da aka yi yunkurin jefa
jihar ciki.
Kwamishinan ya bayyana irin kokarin da Jihar Yobe ke yi karkashin
Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam wajen kula da rayukan daliban makarantu
da ke Jihar don haka ya nemi iyayen yara da cire kowane irin shakku a
zukatansu dangane da kiyaye lafiyar yaransu su ci gaba da kokartawa
wajen tura yaransu makarantu don neman ilimi kamar yadda suka saba.
Dokta Muhammad Bello ya kuma kirayi jama\’a da su kwantar da hankulansu
tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum kana su ci gaba da yin
watsi da farfagandar da ka iya fitowa daga bakin wasu shedanu marasa
kishin kasa.
A wata mai kama da haka kuma hukumar kula da ba da ilimi bai daya
(UBEC) a Jihar ta Yobe  ta ziyarci wasu makarantu a fadar jihar da ke
garin Damaturu da zimmar kawar da duk wani dar-dar daga zukatan
dalibai da malamansu dangane da cewar wai wasu mutane na shiga
makarantu don allura a ka da kasan cibiya ga dalibai maza da mata.
Da yake bayani dangane da wannan ziyara tasu, Sakataren hukumar Alhaji
Shettima Buji ya roki iyaye da jagorin daliban ne da su yi watsi da
irin wannan farfaganda da su ci gaba da tura yaransu makaranta don
daukar darasi kamar yadda suka saba. Kana ya kuma nuna juyayinsa
dangane faruwa hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here