Wasu ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mata Uku A Adamawa

0
825

Rabo Haladu Daga Kaduna

WASU da ake kyautata zaton ‘yan Boko-Haram ne suna ci gaba da satar mata a
Karamar Hukumar Madagali da ke cikin jihar Adamawa, kamar yadda suka sake
sace wasu mata uku jiya a kauyen Magar, lamarin da Mista Adamu Kamale dan
majalisar wakilan tarayya da ke wakiltar yankin ya tabbatar Rahotanni na
cewa wadannan ‘yan bindiga masu tada kayar-baya sun yi awon gaba da
‘yan mata uku a kauyen Magar da ke cikin karamar hukumar Madagali a
arewacin jihar Adamawa yayin da suka je aiki a gona.
Magar dai nada tazaran tafiyar kilomita 25 ne daga Gulak hedikwatar
Karamar Hukumar Madagali, wacce aka kwato daga hannun \’yan Boko
Haram a shekarar 2015.
Kodayake kawo yanzu, duk kokarin ji daga bakin kakakin rundunan soji ta
28 dake Mubi, Manjo Badare Akintoye abun ya ci tura don ko na ta buga
wayarsa ba ‘a dauka ba,to sai dai kuma dan majalisar wakilai da ke wakiltar
Madagali da Michika, Mista Adamu Kamale ya tabbatar da lamarin inda ya
bayyana halin zulumin da suke ciki a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here