BAI KAMATA A RIKA SAMUN RASHIN JITUWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA BA-OGOMO PENGANA

0
607
Isah Ahmed, Jos

MAI martaba Ogomo Pengana dake karamar hukumar Bassa a Jihar Filato, Esua Mamman Shayang ya bayyana cewa sam bai kamata a rika samun rashin jituwa tsakanin manoma da fulani makiyaya ba. Ogomo Pengana ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, a fadarsa dake garin Jingir.

Ya ce babbar matsalar da take damunsu ita ce rikice-rikicen  fulani makiyaya da manoma. Ya ce ya kamata manoma da fulani makiyaya su sasanta junansu, kada a rika samun  fitina a tsakaninsu.

 ‘’Bai kamata manoma su rika sanya wuta bayan sun kwashe amfanin gonakinsu ba. Duk manomin da ya gama kwashe amfanin gonarsa ya bar fulani  makiyaya su kai shanunsu  su ci karan da aka bari. Kuma yadda wasu fulani makiyaya suke yi, na sanya dabbbobi a gonakin da ba a gama kwashe amfanin gona ba, bai kamata ba.

Ogomo Pengana ya yi bayanin cewa akwai dangantaka tsakanin manoma da fulani makiyaya, domin manoma da Fulani makiyaya dukkansu suna daji ne. Ya ce makiyayi ba zai dauki dabobinsa ya kai birni ba, haka shi ma  manomi ba zai yi noma a cikin birni ba. Don haka akwai dangantaka tsakanin manoma da fulani makiyaya.

Hakazalika ya ce makiyaya suna yi wa manoma taki su kuma makiyaya shanunsu suna cin kararen da manoma suka bari.  Don haka ya yi  kira ga manoma da Fulani makiyaya su rika hakuri da junansu su zauna lafiya.

Ogomo Pengana ya gargadi manoma kan su guji  fitar da  kayayyakin amfanin gonar da suka noma  suna sayarwa  barkatai, musamman a wannan  lokacin kaka. Ya ce ya kamata manoma su yi tunani kan kayayyakin amfanin gonar da suka noma su ajiye abin da za su ci, da abin da zasu yi noma, na damina mai zuwa daga nan sai su biya bukata da sauran kayayyakin amfanin gonar da suka noma.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar Nijeriya kan mu koma ga Allah, idan muka yi haka za mu sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here