Jami\’ar Katsina Za Ta Dauki Masu Kama Macizai Aiki

0
712

Rabo Haladu Daga Kaduna

JAMI\’AR Umaru Musa \’Yar\’adu ta Jihar Katsina ta bayar da aikin kame macizai daga makarantar
Babban jami\’in makarantar mai lura da dalibai, Dokta Suleiman Kankara, shi ne ya tabbatar da hakan.
Dokta Kankara ya ce duk da cewa masu kama macijin ba su dade da fara aiki ba, jami\’ar ta
dade tana shirin ta dauke su  aiki.
Ya ce dama dai a duk lokacin da aka samu maciji a makarantar a kan kira masu kama maciji ne
don su taimaka, amma yanzu za a dauke su aiki ne na kodayaushe.
Macizai na sarar fiye da mutum miliyan biyar duk shekara – WHO
A makon jiya ne dai maciji ya kashe wata budurwa tana dab da kammala karatunta a jami\’ar.
Zainab Umar, daliba ce wacce take shekarar karshe a fannin nazarin tattalin arziki ta jami\’ar
Umar Musa \’Yar\’adua ta Jihar Katsina kafin ta rasu.
Wata sanarwa daga hukumar jami\’ar ta ce, maciji ya sari Zainab ne ranar Juma\’a kuma an yi mata
magani a asibitin da ke makarantar.
Sanarwar da jami\’ar hulda da jama\’a ta makarantar Fatima Sanda, ta sanya wa hannu ta
ce a ranar Asabar ne iyayen marigayiyar suka dauketa daga jami\’ar zuwa gida don yi mata maganin gargajiya. Amma sai Allah ya yi mata rasuwa a ranar Litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here