RUWAN WUTAN SOJIN SAMA YA RUTSA DA FIRDAUSI UWARGIDAN  SHUGABAN BOKO HARAM

0
1217
Daga Usman Nasidi
RUNDUNAR sojin saman ta bayyana cewar ruwan wutar da ta yi ya rutsa da uwargidan Shekau duk da cewar har yanzu tana kokarin tantance gawar Firdausi.
Kamar yadda muka kawo muku rahoton kaddamar da ruwan wuta da hukumar sojin sama ta yi a wasu daga cikin maboyar mayakan kungiyar Boko Haram.
Rahotanni na nuni da cewar cikin wadanda suka rasa ransu har da uwargidan shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau.
Ruwan wutar sojin sama a maboyar mayakan kungiyar Boko Haram ya hallaka matar Shekau Firdausi
Sanarwar da rundunar sojin saman ta saki, ta bayyana cewar ruwan wutar da ta yi ya rutsa da uwargidan Shekau din ne yayin da take wakiltarsa a wani taron manyan kwamandojin kungiyar a daya daga cikin maboyar tasu.
Sojojin sama sun yi luguden wuta a maboyar mayakan kungiyar Boko Haram da ke Durwawa daura da Urga da ke Konduga a ranar 19 ga wannan watan.
Harin na hukumar sojin sama dai ya hallaka mayakan kungiyar Boko Haram da dama.
Hukumar sojin ta bayyana cewar har yanzu tana kokarin tantance gawar Firdausi daga cikin ragowar gawarwakin mayakan kungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here