GWAMNATIN KADUNA TA BUKACI AL\’UMMA DA SU KARA MARA MATA BAYA DON KAWAR DA CUTAR POLIO

0
736
Daga Usman Nasidi
A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira da al\’ummar jihar da su ci gaba da mara wa gwamnatin baya dan guje wa sake bullowar cutar Polio
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar cewar akalla shekaru biyar kenan ba a sami bullowar cutar Polio ba a ko ina a jihar. Jihar Kaduna tana daga cikin jihohin da ke Arewacin Najeriya 19 da ta samu nasarar magance wannan cuta.
Shugaban ma’aikatar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko Hadiza Balarabe ne ta fadi haka a Kaduna wajen tattaki da aka yi a jihar domin ranar Polio na duniya.
Ta ce tun a watan Disemba na shekara 2012 ba a sake samun labarin cutar ba a jihar Kaduna.
A karshe ta yi kira ga ‘yan jihar da su ci gaba da mara wa gwamnatin jihar baya don ganin hakan ya dore

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here