WASU DALIBAI SUN FARA ZUWA DAKIN JARABAWA DA BINDIGOGI – Inji Hukumar WAEC

0
720
Daga Usman Nasidi
MAGATAKARDAR hukumar tsara jarrabawa ta WAEC, Dakta Iyi Uwadiae, ya koka da muguwar dabi\’ar wasu daga cikin dalibai masu rubuta jarrabawar gama sakandire ta WAEC ta ba wa jami\’an hukumar masu saka ido a kan jarrabawa kwaya, musamman a makarantu masu zaman kan su.
Magatakardan ya yi wannan korafi ne a Legas yayin bayyana shirin yin wani taro a kan magance magudin jarrabawa a ranakun 19 da 20 ga watan nan.
Uwadiae, ya ce hukumar WAEC ba zata nemi izinin gwamnati domin ba wa jami\’an hukumar makamai ba, sai dai kawai su jawo hankalin gwamnati da kuma jama\’a a kan hadarin da hukumar da jami\’anta ke ciki.
\”Lamarin satar amsa a yanzu ya dauki wani sabon salo saboda lamarin har ya kai da barazanar rayukan ma\’aikatanmu.
Za mu iya kwatanta lamarin da irin yadda masu fasa kwabri ke hallaka jami\’an hukumar kwastan, dalilin da ya sa dole gwamnati ta ba wa jami\’an kwastan din bindigogi.
Sai dai mu a hukumar WAEC ba za mu bukaci a ba wa jami\’anmu bindigogi ba sai dai mu sanar da duniya cewar dalibai a wasu makarantu masu zaman kan su na shiga dakin jarrabawa da bindiga ba ya ga zuba kwaya a cikin abin shan jami\’anmu masu sa ido a kan jarrabawa\”. inji Uwadiae.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here