Matasan Kaduna Sun Gargadi Sanata Shehu Sani

    0
    1013

    Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

    GAMAYYAR kungiyoyin matasa masu zaman kansu karkashin jagorancin Kwamared Zubairu Muktar da Kwamared Richard Augustine sun kara jawo hankalin Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani a kan ya hanzarta saka wa takardun da aka aike wa majalisar, don Jihar Kaduna karkashin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i ta ciwo bashin bankin duniya domin yi wa Jihar ayyukan raya kasa.

    Su dai wadannan gamayyar kungiyoyi karkashin jagorancin Kwamared Zubairu Muktar sun tabbatar wa manema labarai a Kaduna cewa suna tunatar da Shehu Sani ne a matsayinsa na shugaban kwamitin kula da bashin kasashen waje a Majalisar Dattawa ya dace ya yi hanzarin sa wa takardun Kaduna da ke gabansa domin a samu sukunin karbo bashin bankin duniya.

    A cikin takardar da suka raba wa manema labarai a Kaduna sun bayyana cewa hakika sa wa takardar cin bashin nan kawai ya rage wa Shehu Sani idan kuma ba haka ba za su yi gangamin matasa suje Majalisar Dattawan domin nuna masu cewa su a matsayinsu na talakawan Jihar suna goyon bayan Gwamna El- Rufa\’i ya ciwo bashin ta yadda za a samu sukunin gudanar da aiki ga jama\’a.
    \”Za mu wayar wa da dimbin matasa kai domin tafiya zuwa Abuja mu mamaye majalisar ta yadda duniya za ta san cewa mutanen Kaduna na son a ciwo wannan bashin, don haka Shehu Sani ya sa wa takardar nan hannu kawai\”.

    Matasan sun kuma yi kira ga Sanatan da ya cika alkawarin da ya yi wa jama\’a na idan an ba shi kudi a majalisar zai zo ya kira mutane a baje a faifai, saboda kamar yadda matasan suka ce Shehu Sani a yanzu sabanin alkawarin da ya yi wa jama\’a kawai yake aiwatarwa game da batun kudi.

    \”Ta yaya Sanatan da ke wakiltar mutanen Kaduna ta tsakiya zai ki sa hannu a takardun Jihar Kaduna amma kuma tuni ya aiwatar da hakan ga wasu jihohin kasar nan, ko dai akwai Lauje cikin nadi ne? da Shehu Sani ba ya son a yi wa mutanen Kaduna aiki?.

    Ya dace Sanata Shehu Sani ya yi koyi da sauran takwarorinsa na majalisar da suke kokarin kawo wa jama\’arsu abin alkairi domin ci gaba, amma ba irin yadda Sanata Sani yake kokarin aiwatar da son zuciya ba.

    Matasan sun kuma aike da wani sako ga Shehu Sani kan cewar ko da shi Malam Nasiru ne ya fito domin sake tsayawa takara a shekarar 2019, to dole sai abin da mutanen Kaduna sama da miliyan sha biyu suka yanke hukunci don haka ga Shehu Sani ya fara neman hanyar sasantawa don yin tsarin ban gishiri in ba ka manda ga batun takararsa ta Sanatan Kaduna ta tsakiya a 2019 tamkar dibar ruwa ne a cikin burmamme ko kuma tsohon kwando kuma ruwan daga kogi ai zai zama abin dariya kawai.

    Sanata Shehu Sani ya dace ya sani cewa Jihar Kaduna ce ta fi dacewa ta karbo wannan bashin na bankin duniya saboda idan an yi la\’akari da jihohin da ya sanya wa hannu za a ga hakan, domin a cewar matasan sun samu sahihan alkalumman yawan jihohin da suka samu amincewar majalisar da kuma wadanda ake sa ran za su samu amincewar majalisar da Shehu Sani ke ciki a yanzu.

    Gamayyar kungiyoyin matasan masu zaman kansu sun shaida wa manema labarai a Kaduna cewa suna magana ne da yawun akalla mutane miliyan sha biyu da akasarinsu talakawa ne da ba su da bakin magana ko samun hanyar da za su yi magana, saboda haka kada fa Sanata Shehu Sani na aiwatar da aikin da ke zaman tamkar shi ba ya kishin jama\’ar Jihar Kaduna musamman ta wannan fuskar amincewa da takardun karbo bashi daga kasashen ketare.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here