\’Yan Kunar Bakin Wake Biyu Mata Sun Bakunci Barzahu

0
710

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

RAHOTANNI daga Jihar Borno na arewacin tarayyar Nijeriya sun tabbatar da cewa \’yan kunar bakin wake biyu mata sun mutu a wata mashigar hanyar a cikin birnin Maiduguri.

An dai tabbatar da cewa \’yan matan biyu sun mutu ne sakamakon tayar da Bam da wata \’yar kunar bakin waken ta yi inda kuma jami\’an tsaro suka samu nasarar harbe mai kokarin kai hari ta biyu.

An dai ruwaito cewa jami\’an tsaro na cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun yi maganin duk wani mai kudiri irin wannan ko mai kama da shi.

Harin dai ya faru ne a daren jiya Lahadi kuma an shawarci jama\’a da su ci gaba da aiwatar da harkokin su kasancewar hukumomi na ci gaba da ganin komai ya tafi daidai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here