An Killace Mutune 60 A Kano Saboda Kyandar Biri

0
734

Rabo Haladu Daga  Kaduna

HUKUMOMIN lafiya a jihar Kano , sun ce an killace mutum 60 bayan da suka yi mu\’amala da wani
mara lafiya da ake zargin ya kamu da cutar kyandar biri.
A karshen makon nan ne kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Kabir Getso, ya ce: \”an gano alamun
cutar ne a tare da mara lafiyar, sai dai muna zargin cewa tasa cutar ta fi kama da farankama
maimakon kyandar biri.\”
A wata hira da ya yi da manema labarai  ya yi watsi da zargin da ake masa cewa bai dauki halin da mara lafiyar ke ciki da muhimmanci ba.
Ya ce ba za mu tabbatar da cewa yana dauke da cutar ba har sai an dawo da sakamakon jini da
aka kai babban birnin tarayyar  Abuja.
Dokta Getso ya ce an samu bullar cutar kyadar biri a jihohi 11 daga cikin 36 na kasar, kuma mutum
94 ne ake zargin sun kamu da ita, sai dai shida daga cikinsu ne kawai aka tabbatar sun kamu.
A farkon wannan watan ne wani jami\’in lafiya a jihar Bayelsa  ya ce ana samun cutar ne daga jikin birrai da sauran dabbobin daji kamar bera da kurege da barewa.
Ana bincike ko cutar kyandar birrai ta je Kano, Hukumomin lafiya a Najeriya sun yi ta gargadin
jama\’a da su guji cin naman biri da sauran naman daji.
Ministan lafiya  Isaac Adewole, a wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan, ya ce duk da cewa ba a san maganin cutar ba, to babu wani abun daga hankali don ba mai yin muguwar illa ba ce.
Sai dai ya shawarci al\’umma da su dauki matakan kariya kamar gujewa shiga cunkoson jama\’a.
Ya ce cutar na cikin rukunin cututtuka da suka hada da farankama da agana da ciwon \’yan rani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here