Wamakko Ya Tsallake Rijiya Da Baya

    0
    778

    Rabo Haladu Da Mustapha Imrana Daga Kaduna

    DAN Majalisar dattawan  daga jihar Sakkwato ya tsallake rijiya da baya ranar Lahadi da daddare,
    bayan wani sashe na gidansa ya rufta.
    Mai magana da yawun Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alhaji Bashir Mani, ya tabbatar wa
    da manema labarai  afkuwar lamarin, amma ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni.
    Ya ce lamarin ya faru ne jim kadan da ficewar Sanata Wamakko daga gidan wanda ke a
    unguwar masu-hannu-da-shuni ta Gawon-nama; bayan kammala wata ganawa da \’yan siyasa da ya yi a gidan.
    Sai dai wata majiya daga iyalan Sanata Wamakkon ta ce yana cikin gidan lokacin da abun ya faru, sai dai ba a sashen da yake ba ne ruftawar ginin ta afku.
    \”Hakan ne ya sa ba a fi minti goma ba sai ga Gwamna Aminu Tambuwal ya iso gidan da sauri
    saboda yadda labari ya bazu cewa ginin ya rufta da shi a ciki,\” in ji wani makusancin tsohon gwamnan na jihar Sakkwato.
    Alhaji Bashir Mani ya ce babu kowa a sashen ginin da ya rufta din lokacin da lamarin ya faru domin ana gyaran sashen ne.

     

     

     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here