An Kashe Mutum Shida A Jihar Adamawa

0
730

Rabo Haladu Daga  Kaduna

MUTANE shida da suka hada da jami’an  tsaro suka rasa rayukansu sanadiyar rikincin da ya barke tsakanin Fulani makiyaya da manoma a karamar hukumar Yola ta Kudu cikin jihar Adamawa
Kawo yanzu dai mutane shida ne rahotanni suka bayyana cewa sun mutu ciki kuwa har da jami’in dan sanda, da yan banga biyu a wani rikici da ya barke a tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu manoma a cikin karamar hukumar Yola ta kudu dake tsakiyar jihar Adamawan.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, yace shi da kansa ya ga gawar dan sanda dayan da aka kashe.
To sai dai yayin hada hancin wannan rahoto, Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar SP Othman Abubakar ya ce mutum guda ne aka kashe, yayin da aka baza jami’anta don cafko mabarnatan.
Haka shima dai da yake karin haske, Kakakin rundunan jami’an tsaron farin kaya ta sa-kai,Suleiman Baba ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here