Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga daukacin \’yan Nijeriya da kada su amince da duk wani shiri ko bukatar da wani ko wasu gungun jama\’a ke yi na kokarin wargaza kasar na kasancewar ta kasa daya al\’umma daya.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a wajen kwarya-kwaryar taron tunawa da \’yan mazan jiya da suka sadaukar da kansu domin ganin Nijeriya ta ci gaba da zama kasa daya.
Ya ce dukkan masu kururuwar tayar da tashin-tashinar raba kasa ba masu son zaman lafiya ba ne.
Ya kuma bukaci daukacin \’yan Nijeriya, masana\’antu da dukkan masu hannu da shuni da su sayi bajen tunawa da \’yan mazan jiya domin taimaka wa kungiyar \’yan mazan jiya.
A wajen taron an yi bikin rantsar da sabon sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Gida Mustapha da shugaba Buhari ya nada kuma sakataren ya kama aiki nan take.