Rabo Haladu Daga Kaduna
DAYA ga watan Nuwamba dokar hana kiwon dabbobi a jihar Binuwai za ta fara aiki, amma kungiyar
Fulani makiyaya tace ba zata lamunta da ita ba muddin gwamnatin jihar ba ta ware musu wuraren kiwo ba
Kungiyar Fulani makiyaya a Najeriya, Miyetti Allah, ta koka da sabuwar dokar hana yawon kiwo da dabbobi da gwamnatin jihar Binuwai ta ayyana.
Daga ranar daya ga watan Nuwamban nan mai zuwa, sabuwar dokar za ta fara aiki a jihar. Fulani makiyaya sun ce dokar ta saba wa ‘yancin walwalarsu a matsayinsu na kasancewa ‘yan Najeriya.
To amma kuma gwamnatin jihar ta ce ta dauki matakin ne domin shawo kan yawan rikicin da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma a jihar.
A wani taron manema labarai da mataimakin shugaban kungiyar Makiyaya ta Najeriya wato Miyetti
Allah, Alhaji Useni Boso ya kira a Minna, jihar Neja, ya ce sun yi hannun riga da dokar kuma ba su yarda da ita ba. Maganin matsalar shi ne a yi makiyaya da mashaya domin dabbobi.
Hakan yakamata don’ Samar da zaman lafiya.