\’Yan Kasuwa Ku Zo Mu Ba Ku Shawarwarin Hanyoyin Da Gwamnati Ta Amince Da Su ___ Olusemine Kayode

0
710

Rabo Haladu Daga Kaduna

KWANTIROLA Olusemine Kayode  mai kula da Katsina da Kaduna ya jinjina wa ma\’aikatan da ke aiki a karkashinsa saboda sadaukar da kai na yin aikin tukuru  domin kawar da bin hanyoyin da ba bisa ka\’ida ba a dukkanin bodojin yankin da suka hada Jibiya, Kongwalan, Baban Mutum na shigo da shinkafa ,  man talatalo, ba bisa ka\’ida ba Inda ya ce \’yan kasuwa ba abokan gabar kwastan ba ne abokan aiki ne amma su bi ka\’idar da gwamnati ta gindaya masu abun da ya shigar masu duhu su zo mu zuana domin mu ba su shawara.
Kwantirolan ya yi wannan bayyani ne a yayin zantawarsa da manema  labarai  lokacin da ya kai  ziyarar ba za ta a \”yakokin da ke jihar ta Katsina. Inda suna ta kokarin dakile yin fasa-kwari, ya ce fatarsu shi ne al  \’ummar Nijeriya su fahimci irin hatsarin da suke shiga  wajan gudanar da aikin nasu.
Olusemine Kayode ya ce ba za su yi barci ba har sai sun tabbatar da cewa \’yan kasuwa sun daina  shigo da kayayyaki da aka hana shigo da su irin su shinkafa da man-toki da suke  da matsala ga  gwamnatin tarayya  da al\”ummar kasar nan.
Ya kara da cewa idan har al \’ummar kasar nan suka ba su goyan baya ta fallasa duk wata hanya da \’yan fasa kwauri ke amfani da ita wajan cin karensu babu babbaka lalai ne za mu kawo karshen fasa-kwauri a duk fadin kasar nan .
A karshe ya yi kira ga duk jami \’an hukumar kwastan da su ji tsoran Allah domin su sauke amanar da suka daukar wa kansu da \’yan kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here