Za A Biya Diyyar Naira Biliyan 88 Na Yakin Biafra

0
688

Rabo Haladu Daga  Kaduna

GWAMNATIN Najeriya ta amince za ta biya wadanda yakin Biafra ya shafa diyya da kuma kwashe ragowar abubuwan fashewar da suka a rage a yankin da aka yi yakin basasar a karshen shekarun 1960.
Kasa za ta dauki matakin ne bayan an cimma wata yarjejeniya da kotun Raya Tattalin Arzikin Kasashen yankin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta jagoranta.
Takardun kotun sun ce akwai fiye da bama- bamai 17,000 da aka gano a yankin. (kimanin Dala Miliyan 245) a matsayin diyyar ga wadanda yakin ya shafa, shekara 47 bayan kawo karshensa. yakin  ya shafa a jihohi 11 a yankin kudu maso gabashi, da kuma yankin arewa maso tsakiya wuraren da
yakin ya fi shafa.
Ragowar kudin za a yi amfani da su ne wajen kwancewa da share nakiyoyin da suka rage a yankin, da kuma wajen gina makarantu da kotuna da coci-coci da kuma masallatai a yankunan.
Fiye da mutum miliyan daya ne suka rasa rayukansu sanadiyyar yakin, galibinsu saboda yunwa da kuma cututtuka a yakin da aka yi tsakanin shekarun 1967 zuwa 1970.
An fara yakin ne biyo bayan ayyana ballewa da yankin Biafra daga Najeriya, wadanda galibi \’yan kabilar Ibo ne suka jagoranta.
A \’yan shekarun nan, jagoran kungiyar da ke fafutikar kafa kasar (IPOB) Nnamdi Kanu yana kafa hujja da rashin biyan diyyar wajen sake farfado da fafutikar ballewar yankin daga Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here