Wasu Kusoshin Jam’iyyar APC Ba Su Halarci Taronta Ba

  0
  694

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  SHUGABANNIN jam\’iyyar APC mai mulki Injiniya Buba Galadima da Alhaji Atiku Abubakar na cikin manyan kusoshin jam’iyyar APC da ba su halarci taron kolin jam’iyyar ba da aka yi a Abuja ba.
  Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi taron kolinta ba tare da halartar wasu da ake ganin kusoshinta ne ba.
  Daya daga cikinsu, Injiniya Buba Galadima da bai kasance a taron ba, ya yi zargin cewa an hanashi gayyata zuwa taron ne. Amma sakataren jam’iyyar na kasa Mai Mala Boni ya ce a tasa sanin an gayyaci Buba Galadima zuwa taron.
  Haka ma har aka waste daga taron ba’a ga tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ba a taron.
  Dokta Abubakar Umar Kari ya ce rashin kasancewar Alhaji Atiku Abubakar a taron da walakin, wai goro a miya.
  To saidai sakataren jam’iyyar na kasa ya ce rashin kasancewar irinsu Atiku Abubakar a taron bai nuna alamar akwai matsala ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here