Rabo Haladu Daga Kaduna
MA\’AIKATAN kananan hukumomi a jihar Katsina fiye da dari shida ne suka gurfanar da gwamnatin jihar a gaban kotun kula da hakkokin ma’aikata ta Najeriya dake Kano saboda dakatar da albashinsu da ta yi kimanin watanni ashirin da suka gabata, suna kuma neman diyyar Naira Miliyan dari biyar.
Tun a watan Afrilun bara ne gwamnatin jihar ta Katsina ta ba da umurnin dakatar da albashin wasu daga cikin ma’aikatan da ke aiki a karkashin majalisun kananan hukumomi talatin da hudu na jihar saboda zargin kaurace wa wuraren ayyukan su.
Wadanda wannan matakin ya shafa sun kai kimanin dari shida da goma sha biyar.
Sai dai ma’aikatan sun musanta wannan ikirarin na gwamnati. Suna masu fadin cewa, gwamnatin na
neman muzguna wa rayuwarsu ne kawai.
Bayan duk wani yunkuri na daidaitawa tsakanin bangarorin biyu ya ci tura, ma’aikatan sun gabatar da batun ga kotun kula da hakkokin ma’aikata ta tarayya dake nan Kano, domin ta sa gwamnatin jihar Katsina ta ci gaba da biyan su albashi kuma ta basu ariya na watanni ashirin da suka gabata.
Sunayen ma’aikata biyar ne dai ke jikin takardar karar a matsayin wakilan sauran dari shida da goma, al’amarin da ya sanya lauyan gwamnati Barrista Abu Umar ke cewa, tun da ma’aikatan biyar sun nuna kananan hukumomin da suka dauke su aiki, ya kamata a zayyana sunayen sauran ma’aikatan don kotu ta san da su.
Sai dai lauyan da ke kare ma’aikatan Barrista Kamalu Umar ya yi martani a kan haka, ya ce ba haka batun yake ba, saboda dokar kotu ta ba da wannan damar.
Yanzu haka dai alkalin kotun kula da hakkokin ma’aikatan ta Kano mai shari’a E.D Esele ya dage sauraron
shari’ar zuwa ranar 7 ga watan gobe na Disamba.