Izala Nake Kira Da Ta Taimaka Mani Da Kafafuwan Roba

0
823
ZUWA GA KUNGIYAR JIBWIS.
Salam, Edita barka da aiki kuma Allah ya kara maku nasara baki daya. Bayan haka zan yi amfani da wannan fili domin yin roko ga kunguyar JIBWIS da ta taimaka ta sanya ni cikin shirnta na tallafa wa mutane da kafafuwan roba sakamakon yanke tawa da aka yi sanadiyyar wani ciwo.
Ina fata wannan kungiya mai albarka za ta duba wannan kuka nawa ta sanya ni cikin jerin mutanen da za ta taimakawa ta yadda ni ma zan ci gaba da tafiya kamar yadda na ga an yi wa mutane masu tarin yawa kuma domin Allah. Allah ya kara albarka cikin wannan kungiya, ya yi mata sakayya ta alheri bisa taimaka wa al\’umar Annabi Muhammad da take yi tun kafata.
Malam Harisu Abdullahi Kofar Fadar Agoran Zuba, Zuba, Abuja.
08035741428

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here