Karancin \’Ya\’yan Goro Shi Ne Ya Kawo  Tsadarsa A Wannan Lokaci- Dillalan Goro.

    0
    1001
    Jabiru A Hassan, Daga  Kano.
    MASU sana\’ar sayar da goro da kuma dillancin sa a kasuwannin goro na Ujile da kuma Mariri sun bayyana cewa karancin \’ya\’yan goro  a  guraren da ake noman sa shi ne dalilin tsadarsa a wannan lokaci.
    Sannan sun sanar da cewa saboa wannan dalili ya sa suka fadada zuwa neman sa har a wasu kasashe na Nahiyar Afirka irin su Ghana da Kwadebuwa watau Abidjan da kasar Gini Konakary da Kamaru  bayan wanda ake da shi a cikin gida kamar Shagamu da Ile-ife da Ore ta jihar Ondo da Auwode da sauran inda ake jarraba noman sa.
    Haka kuma dillalan goron sun sanar da cewa kafin su kai kaya zuwa kasuwanni da hannayen diloli suna caukar lokaci a kan hanyoyi da inda ake sauke shi saboda tantance shi da jami\’an tsaro keyi don tabbatar da cewa komai yana tafiya cikin nasara, inda kuma suka jaddada aniyar su ta ci gaba da samar da goron kamar yadda suka saba.
    A kasuwar goro ta Ujile da ke Birnin Kano, wakilinmu ya zanta da wani dattijo wanda kuma ya kai shekaru saba\’in yana sana\’ar sayar da goro watau  Alhaji na Usama wanda ya yi tsokaci kan yadda sana\’ar goro ta sami asali daga tashar jiragen kasa watau reluwe zuwa Ujile sakamakon ganin an hade  wajen sayar da shanu da dalar gyada da kuma ita kanta Ujile a zamanin sarkin Kano Sunusi kakan sarki Sunusi na yanzu.
    Bugu da kari ya bayyana cewa kaauwar goro ta Ujile ita ce ta haifi kasuwar goro ta Mariri kuma a cewar sa har yanzu ana harkar goro a gurin kuma guri ne mai tsohon tarihi tun zamanin dattawan Ujilen goro irin su Alhaji Dan mai wanki da Alhaji Gambo na Alhaji Alin Mu\’awuya da kuma Alhaji Dangado wadanda suka yi fice a sana\’ar goro.
    Su ma shugabannin kungiyar \’yan goro ta Ujile irin su Alhaji Baba Sa\’idu da Alhaji Bashir Dan Dalama da Alhaji Sani kasa da kuma Alhaji Balarabe Koki sun nunar da cewa sana\’ar goro tana da albarka ga shi kuma yanzu tana da martaba saboda muhimancin sa ga al\’uma.
    A kasuwar goro ta mariri kuma,  daya daga cikin shugabannin kasuwar Alhaji Nasiru Husaini Dan Gongola ya ce an dade ba a ga darajar goro irin ta bana ba sakamakon yadda itatuwan goro a ciki da wajen kasar nan suka sami karancin haihuwa wanda hakan ce ta sanya  ake  zuwa kasashe  daban-daban nemansa.
    Sannan ya yi kira ga gwamnati da ta rika saurin tantance motocin daukar goro a kan iyakokin kasar nan ganin cewa shi goro abu ne da ba ya son tsaiko don gudun lalacewa, sannan ya bukaci gwamnatin jihar Kano da karamar hukumar Kumbotso da su hada hannu wajen kara inganta wannan kasuwa ta mariri musamma katangeta da sanya mata fitilu a kan titunan cikinta ganin yadda a kullum mutane sama da  dubu biyar suna gudanar da kasuwanci a wannan guri.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here