Matashi Dan Kato Da Gora Ya Harbe Kansa Wajen Atisaye

0
695
Daga Usman Nasidi

WANI matashi Dan Kato da gora a jihar Katsina ya hallaka kansa a yayin da yake kokarin gwajin maganin Bindiga inda ya bar baya da kura.
Dan ƙato da goran na ƙungiyar Isan Gona mai suna Ahmadu Mai Kare da ke a unguwar Gidan Jimina, da ke a ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina ya harbe kansa ne a ƙoƙarinsa na nuna wa duniya cewa shi fa ya ci ya sha saboda haka bindiga ba ta cinsa.
Lamarin dai ya faru ne a yayin da ake gudanar da bikin ƙaddamar da sababbin ɗauka a ƙungiyar, inda ‘yan ƙato da gorar suka taru a gidan shugabansu, Sama’ila Rabi’u, a ƙauyen Dubul da ke ƙaramar hukumar Matazu, inda bisa al’ada, ‘yan ƙungiya za su bi bayan juna wajen nuna bajinta.
Ko da Mai Kare ya shiga tsakiyar da’irar abokan aikinsa, sai ya fiddo da wani guru ya ɗaura kana ya sanya laya, ya kuma ci gaba da wasu gwalangwalantu kafin ya ɗaga bindigar ya gwada ta a kansa, ya dana kunamar bindigar ya kuma saki.
 Ko da sakin kunamar bindigar, sai ji kake daaraaam, nan take Mai Kare ya faɗi matacce.
Mutuwar Mai Kare ta sanya da dama daga cikin waɗanda ke wajen sun ranta a na kare, inda ‘yan uwa da abokansa ne kaɗai suka tsaya a kan gawarsa.
Kakakin hukumar ‘yan sandar jihar Katsina, DSP Isah Gambo ya tabbatar mana da wannan labari, inda ya bayyana cewa ‘yan sanda sun shiga bincike a kan faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here