Mun Kafa Kungiya Ne Domin Bunkasa Noman Tumatur- Alhaji Dabo Adamu Zaura

0
960
Jabiru A Hassan,  Daga Kano.
MANOMAN tumatur da ke yankin Zaura da kewaye sun kafa wata kungiya domin kara bunkasa nomansa da kasuwancinsa da kuma sarrafa shi ta yadda kowane manomi zai amfana da noman da yake yi.
Wannan bayani ya fito ne daga jagoran kungiyar a zantawar da suka yi da wakilinmu bayan kammala wani taro kan shirin noman tumatur na rani wanda ake shirye-shiryen farawa nan gaba kadan, inda kuma ya fayyace dukkanin tsare-tsaren da suke son aiwatarwa ta karkashin wannan kungiya kafin lokacin noman rani.
Ya ce kafin kafa wannan kungiya ta \” Zaura Tomato Farmers Association\”, sai da suka yi kokarin hada kan manoman tumatur na wannan bangare tare da bayyana masu dukkanin manufofin kafa wannan kungiya ta yadda za ta zamo alheri ga daukacin manoman tumatur da ke yankin kasar Zaura da kewayae da kuma kasa baki daya.
Alhaji Dabo Zaura ya kuma sanar da cewa yanzu noman tumatur ya zamo abin alfahari ga dukkanin masu yinsa walau da damina ko kuma da rani, don haka yana da kyau su kafa wata kungiya mai amfani ga manoman ta yadda za su kara samun yanayi mai kyau na bunkasa noman nasu da kasuwancin sa da kuma nemo hanyoyin sarrafa shi cikin nasara.
Dangane da maganar noman rani kuwa, Alhaji Dabo Adamu ya nunar da cewa akwai wasu kyawawan tsare-tsare da suke yi domin ganin dukkanin manoman tumatur na kasar Zaura da kewaye suna samun dukkain wata kulawa daga gwamnatoci da hukumomin kula da aikin gona da kungiyoyi da kuma kamfanonin sarrafa kayan amfanin gona kamar yadda ake gani a sauran kasashen da suka ci gaba ta fannin aikin noma.
A karshe yayi fatan cewa wanna haxin kai da suka fara zai ci gaba da tafiya cikin nasara saboda yanzu lokaci ya yi na kakkafa kungiyoyin manoma domin ganin an farfado da martabar wannan kasa ta fuskar samar da abinci da kayan sarrafawa ga kamfanoni da masana\’antu na sarrafa kaya amfanin gona ba tare da nuna gajiyawa ba.
Wadanda aka nada domin su jagoranci kungiyar su ne Shehu Babangida a matsayin shugaba sai Tukur Sale mataimakin shugaba da Usman Isa a mukamin sakatare da Alhaji Sunusi Kirya matsayin ma\’aji. Sai Abdu Kirya a matsayin sakataren kudi da kuma Haruna Bello mai binciken kudi.
Sauran jami\’an kungiyar sun hada da Musa Juji Kirya sakataren baki da Musa Juji sakataren tsare-tsare sai Sha\’aibu Yusuf jami\’in hulda da jama\’a da kuma Dauda Abubakar a matsayin mai ladabtarwa.
Bugu da kari, an zabi iyayen kungiya wadanda suke da hurumin tsara tafiyar da harkokin ta kamar Dalha Adamu da Umaru Musa da Usaini Musa da Alhaji Abdu Umari da Alhaji Sa\’idu Adamu da kuma Magaji Idris yayin da shi Alhaji Dabo Adamu Zaura ya kasance jagoran kungiya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here