An Kashe \’Yan Shi\’a Hudu A Kano

0
765

Rabo Haladu Daga  Kaduna

KUNGIYAR \’Yan uwa Musulmi ta mabiya Shi\’a a Najeriya (IMN) ta ce an kashe akalla mambobinta \”hudu\”, yayin da \’yan sanda suka tarwatsa wani tattaki da \’yan kungiyar suke yi a Kano ranar Lahadin nan da ta wuce.
Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya ce suna tattakin Arbaeen ne yayin da al\’amarin ya faru a kan hanyarsu ta zuwa garin Zariya daga Kano. Ya ce cikin mutanen da suka mutu har da mata biyu. Kuma kakakin kungiyar ya ce akwai wadanda suka jikkata da dama.
Kakakin rundunar \’yan sanda ta jihar Kano DSP Magaji Musa ya tabbatar wa da manema labarai  cewa
jami\’ansu sun tarwatsa tattakin \”ba tare da nuna karfin tuwo ba, saboda taron ya saba wa doka.\”
Mun gargadi shugabanninsu kan kada su fito wannan tattakin,\” kamar yadda ya ce.
\’Yan kungiyar suna tattakin ne don tuna wa da halin da jikan Manzon Allah (SAW) Imam Hussain ya shiga a karni na bakwai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here