Har Yanzu Akwai Matsalar Ruwa A Asibitin Waziri Gidado Da Ke Kano

0
749
Jabiru A Hassan,  Daga Kano.
SANANNEN asibitin nan na Waziri Shehu Gidado da ke Kano  yana fama da matsalar ruwa tun lokaci mai tsawo wanda hakan ta sanya tilas sai masu jinyar \’yan uwansu a asibitin suke sayen ruwan leda wato \”pure water\” domin yin amfani da shi kowace rana.
Sannan binciken da wakilinmu ya gudanar a asibitin ya gano cewa a baya an yi ta kokarin samar da ruwa ta hanyoyi daban-daban amma abin bai yiwu ba saboda tsaurin da gurin yake da shi wanda an sha kokarin haka rijiyoyin burtsatse a cikin asibitin amma ba a cimma nasarar hakan ba.
Sai dai a binciken ya gano cewa, ita kanta hukumar asibitin tana  kokari sosai wajen ganin an sami wadataccen ruwa a wannan guri inda ta yi tunanin hada ruwa daga babban bututun da yake bai wa Birnin Kano da kewaye ruwa wanda ya fito daga madatsar ruwa ta Watari da ke Bagwai domin kawo karshen matsalar ruwan da ta dabaibaye asibitin na Waziri Gidado.
Wasu daga cikin masu jinyar \’yan uwan su a asibitin sun shaida wa GTK cewa  ana fama da rashin ruwa a wannan guri ga shi kuma guri ne mai matukar muhimmanci ganin irin aikin da ake yi cikin sa na kula da lafiyar al\’umma ba tare da kasala ba, sannan ita kanta hukumar asibitin tana kokari wajen sayen ruwa a kullum domin saukaka wa majinyata wahalar da suke sha kafin a sami ruwa a gurin.
Hajiya Rabi\’atu Adamu, wadda ta yi jinyar kanwarta ta ce \”gaskiya akwai bukatar gwamnatin Jihar Kano ta duba matsalar da asibitin ke ciki ta rashin  ruwa saboda guri ne babba wanda kuma yake daukar mutane masu yawa a kowace rana musamman mata da kananan yara\”,  sannan ta yi roko ga kananan hukumomin da ke kewayen wannan asibiti da masu iko da su daure su rika kai tankokin ruwa ana juyewa a wani guri domin amfanin al\’umma kamar  yadda ake yi a wasu gurare.
Bugu da kari, wata maras lafiya da ta kwanta a asibitin a yayin ziyarar ta wakilinmu, Malama A\’isha ta  bayyana cewa idan har gwamnatin Jihar Kano da kananan hukumomin da ke kusa da wannan asibiti suka hada  karfi, ko shakka babu za a kawar da matsalar rashin ruwa da ta dade tana ci wa asibitin tuwo a kwarya, inda kuma ta yaba wa manya da kananan ma\’aikatan asibitin na Waziri GIdado saboda kwazon da suke nunawa na kula da marasa lafiya a kodayaushe.
Sai dai Daraktan asibitin Alhaji Kabiru Salisu ya bayyana cewa yanzu haka ana ta kokarin  ganin an kawar da wannan matsala ta rashin ruwa a wannan asibiti, musamman ganin cewa gwamnatin Jihar Kano ita ma a nata bangaren tana kokari kwarai da gaske wajen inganta asibitoci a cibiyoyin kula da lafiya a fadin jihar inda ya ce\” in sha\’Allah za a kammala aikin hada asibitin da babban bututun ruwa wanda ya wuce ta  jikin asibitin domin magance matsalar ruwa a wannan asibiti na Waziri Gidado\”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here