Burina Jami’ar Al- Kalam Ta Yi Gogayya Da Jami’o\’in Duniya…. Inji Farfesa Garki

0
916

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABAN Jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina Farfesa Shehu Ado Garki, ya bayyana cewa Jami’ar tana daga cikin
sauran jami’oin kasar nan da suke bayar da gudummawa wajen bunkasa harkar ilimi a fadin kasar nan wanda
hakan ya sanya mahukunta Jami’ar suka dukufa wajen kara inganta Jami’ar ta bangarori daban-daban.
Farfesa Ado Garki, ya kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba Jami’ar Al- Qalam za ta yi gogayya da sauran
jami’oin duniya wajen koyarda ilimin kimiyya da fasaha.
Ya ce” Babban burina shine Al-Qalam ta zama jami’a kamar sauran jami’oi masu koyar da ilimin kimiyya da fasaha haka kuma ta zama tana gogayya da sauran jami’oin duniya in sha Allah ”
Ya kuma bayyana cewa Jami’ar Qalam ba ilimin addinin musulunci kawai take koyarwa ba; har da sauran kwasa-
kwasan da suka shafi harshen Hausa da Turanci da ilimin koyarwa da kuma kimiyya da fasaha, inda ya ce ba
jami’a ce ta musulmi zalla ba har da wadanda ma ba musulmi ba suna karatu cikinta, a cewarsa, suna bayar da tarbiyya irin ta musulunci.
Da yake bayani dangane da halin da Jami’ar take ciki, Farfesa Garki Ado, ya ce” lokacin da na karbi shugabancin
wannan jami’a kwasa- kwasai guda hudu ake yi amma cikin ikon Allah yanzu muna da kwasa-kwasai guda 18
kama daga darrusan kimiyy da turanci da Hausa da koyar da ilimi koyarwa da sauransu wanda kuma hukumar
kula da jami’o\’in kasar nan NUC ta ba da izinin koyar da guda 13 na dindin-din sauran kuma na wucin gadi ne wanda cikin wannan watan za su zo su duba suka gani kamin su bada izini na din-din-din.
Da yake bayani dangane da kula da lafiyar daliban jami’ar, Farfesa Shehu Ado Garki, ya ce ” mun tanadi dakin
kula da lafiyar dalibai har da ma mata masu juna biyu wanda idan mace haihuwa ta kamata za ta iya haihuwa
a can, haka kuma mun tanadi injinan samar da wuta domin koda an dauke wutar lantarki; haka kuma mun gina
rijiyar burtsa-tsai domin Samar da ruwan sha mai kyau saboda haka mun yi bakin kokarinmu wajen ciyar da jami’ar gaba.
A kan hakan ya bukaci daukacin daliban Jami’ar da su tabbatar da cewa sun bi dokokin Jami’ar domin ganin sun samu abin da kawosu jami’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here