Kungiyar SWAN: Ta Kafa Kwamitin Zabe Na Mutum 3

  0
  856
  MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
  KUNGIYAR marubuta labarin wasanni ta kasa reshen jihar Kuros Riba SWAN  ta nada kwamitin mutum uku da za su gudanar da zaben sababbin shugabannin kungiyar.Matakin ya biyo bayan taro da kungiyar ta saba yi ne a harabar filin wasa na UJ Esuene kuma an dora  masa  alhakin shiryawa da kuma  gudanar da tsabtataccen zabe, an bai wa kwamitin mako biyu ya shirya tare da gudanar da tsaftataccen  zabe.
  Wadanda aka nada su ne kwamared  Vitalis Ugoh, na jaridar  New Nigeria shugaba,  Eme Offiong,wakiliyar gidan radiyon muryar Nijeriya  VON, kana kuma da wakilinmu na kudanci  Musa Kutama na jaridar gaskiyatafikwabo  .
  Da yake nada kwmaitin shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen Kuros Riba Kwamared Albert Andinam, ya ce an ba su wa\’adin mako biyu kacal su shirya zabe wasu shugabannin
  kungiyar ba tare da wani jinkiri ba.
  Kamata ya yi a ce an gudanar da zaben shugabannin kungiyar tun cikin watan jiya to amma saboda mutuwar mataimakin shugaban kungiyar swan ta kasa shiyyar  kudu maso kudu Eddy Bekom aka dage zaben sai a wannan
  lokaci ne aka kafa kwamitin da zai gudanar da shi.
  Haka nan kuma an amince baki daya a taron da Kungiyar SWAN ta yi na masu ruwa da tsaki da kuma shugabannin kungiyar cewa kwamared  Charles Eniang mawallafin jaridar  Glimmer ya  maye gurbin da marigayin  Eddy
  Bekom ya bari.
  Mataimakin shugaba na kasa shiyyar kudu maso kudu domin ya karasa wa\’adin da ya bari jihohin Akwa Ibom da Kuros Riba ne ke da alhakin fitar da wanda zai maye gurbin sai dai lura da cewa marigayin dan Kuros Riba ne shi ke wakiltar jihohin biyu aka nuna Eniang ya maye gurbin nasa duk da su ma \’yan kungiyar na jihar Akwa Ibom suna so su ma a ce wani daga jihar su ne ya maye gurbin marigayin tun da jihar na daya daga cikin jihohin kudu maso kudu 6. Da ake wakilta a kungiyar ta kasa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here