\’Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 11 A Filato

0
781

Rabo Haladu Daga Kaduna

WASU \’yan bindiga sun harbe mutum 11 kusa da Rim da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Filato
Wasu mazauna kauyen ya shaida wa manema labarai, cewa mutanen suna dawowa ne daga kasuwar kauyen
Makera lokacin da lamarin ya auku a ranar Talata da yamma.
Shaidun sun ce an yi wa mutanen kwanton bauna ne a lokacin da motarsu ke dawowa daga kasuwar kauyen.
Har yanzu dai babu wanda ya ta dauki alhakin kai harin. Zuwa yanzu dai jami\’an tsaro ba su sanar da kama kowa game da lamarin ba.
Sai dai kuma hare-haren kabilanci da aka dade ba a samu ba a jihar sun fara dawowa Filato a baya-bayan nan.
Bayan hare-haren sun fara dawowa ne gwamnatin Najeriya ta tura jiragen yaki yankin domin tallafa wa sojin kasa da ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
A baya dai an sha fama da rikice-rikice a jihar ta Filato, al\’amarin da ya yi sanadin rasa dumbin rayuka tare da raba mutane da dama da muhallansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here