MATAKAN DA EL-RUFA’I YA DAUKA KAN MALAMAN MAKARANTUN FIRAMARE YA YI DAIDAI-FARFESA DADARI

    0
    891
    Isah Ahmed, Jos
    FARFESA Salihu Adamu Dadari Malami ne  a sashin bincike da koyar da dabarun noma na jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya kuma mai sharhi ne kan al’amauran yau da kullum. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan matakan da gwamnan jihar Kaduna ya dauka, kan gyara harkokin ilmi a jihar musamman bangaren makarantun firamare,  ya
    bayyana cewa matakan da gwamnan ya dauka sun yi daidai. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
    GTK; A matsayinka na masani kan harkokin ilmi mene ne za ka ce kan kokarin korar dubban malaman makarantun firamare  da ake yi a jihar Kaduna, sakamakon rashin cin jarrabawar da aka yi masu?
    Farfesa Dadari; Maganar gyara harkokin ilmi  da gwamna  Nasiru El’Rufa’i yake yi a jihar Kaduna, ya yi daidai. Domin jihar Kaduna ita ce cibiyar jihar arewa, kuma nan ne aka fara kafa jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jami’ar da tafi kowace shahara a yankin Afrika ta yamma. Saboda haka idan gwamnan jihar Kaduna El’Rufa’i ya ce zai gyara harkokin ilmi a jihar Kaduna, addu’a ya kamata a yi masa.
    Wannan mataki da gwamna El’Rufa’i ya dauka kan gyara harkokin ilmi, musamman  bangaren makarantun firamare ya yi daidai a wajen masu son gaskiya da ci gaba. Amma a wajen wadanda basa  son  gaskiya da ci gaba bai yi daidai ba.
    Domin a baya, an gina makarantun firamare a turbar siyasa, an bi dukkan kauyuka an gina  makarantun firamare. Akwai kauyukan da ba su kamata a gina masu makarantun firamare ba, domin za ka ga wani kauyen bai kai nisan kilo mita daya tsakaninsa da wani kauyen ba, amma an gina masa makarantar firamare. Zaka ga irin wadannan makarantu babu kujeru, za ka sami malamai sama da 20 a rubuce, amma ba sa zuwa aiki. Kuma yawaicin malaman ba sa son zuwa kauyuka, sun fi son su zauna a gari.
    Kuma yawaicin irin wadannan malamai, an dauke su aiki  ne ta hanyar alfarma. Za ka ga manyan mutane sun kawo yaransu sun ce a dauke su aikin koyarwa a makarantun firamare, domin su ci abinci, ba tare da suna da tsarin koyarwar ba. Wadannan malamai ba sa sa ‘yayansu a cikin makarantun da suke koyarwa, suna kai ‘yayansu makarantun kudi ne.
    Wannan matsala ce a kasar nan baki daya, ba  a jihar Kaduna kadai ba. Idan aka tantance malaman makarantun firamare na kasar nan, za a sami baragurbi ne. Don haka idan El-Rufa’i ya ce zai yi gyara kan wannan al’amari bai laifi ba, a wajen wanda yake son ci gaba.
    Tsarin ya lalace shi kuma gwamna El-Rufa’i yana son ya yi gyara, don haka ya dauki wannan mataki. Idan aka dauki malaman nan kan ka’ida, sai su dauki aikin da mahimmanci. Amma a baya, an rika daukar malamai ba bisa ka’ida ba. Za ka ga wani bai iya rubuta sunansa, amma an dauke shi aiki a matsayin malamin da zai je ya koyar a makarantar firamare.
    Wannan abu da El-Rufa’i yake yi daidai ne, domin duk wanda aka dauka bisa ka’ida  zai rike aikin da mahimmanci ya zauna ya yi  tsakaninsa da Allah. Ba mu ce a kori mutane ba, amma bai kamata a dauki mutane aiki ya kasance ba sa yin aikin ba.
    Ya kamata malami ya zamanto mai ilmintar da kansa a kullum ta hanyar karanta jaridu da sauraron rediyo, domin ya san abubuwan da suke faruwa na yau da kullum. Amma yanzu a tambayi malami wane ne shugaban majalisar dattawa ya ce bai sani ba,  bai kamata ba.
    Jarrabawar da aka yi wa malaman nan a jihar Kaduna, ya kamata a tantance wasu a sake nazari. Wadanda basu cancanta ba a sallame su, a dauko wadanda suke da takardar koyarwa.
    Kuma a gyara wa malaman nan  albashinsu  idan ana son su yi aiki, a takaice a rika biyan karamain malami naira dubu 50 a wata. Kuma a tabbatar cewa duk malamin da aka tura wani kauye, ya tafi  wajen. Kada a kara yarda malamai su rika bayar da cin hanci, suna kin tafiya kauyuka don su zauna a gari.
    GTK;  Kwanakin baya gwamnatin ta jihar Kaduna  ta bayyana cewa za ta dauki wasu tsangayoyi na jami’ar jihar, ta kai wasu yankuna na jihar ya ya kake ganin wannan mataki?
    Farfesa Dadari; Idan gwamnan El-Rufa’i ya yi haka ya yi kuskure, domin ko a wajen taron masu ruwa da tsaki na jihar Kaduna da aka yi a kwanakin baya, na fito na fada masa cewa babu yadda za a yi a kasa tsangayoyin jami’a kamar gyada. A duk duniya yin haka ba shi da wani tasiri a fannin ilmin jami’a. Yanzu ana cewa kasa bata da kudi, jihar Kaduna ma ana cewa bata da kudi. Yanzu  ka sanya jami’a a garin Kaduna ka yi zirga-zirgar  daga Kaduna zuwa Lere don duba da wata tsangaya ko ka tafi Birnin Gwari ko ka tafi Zangon Kataf don duba wata tsangaya nawa za ka kashe?. Wadannan kudade da za a rika kashewa basu isa ayi amfani da su a sayi wasu na’urori  da za a sanya a wannan jami’a ba?
    Babu shakka inda aka ajiye wannan jami’a yanzu ya yi kadan, ya kamata a sami wani babban fili kamar muraba’in mil dubu 5 ko  dubu 10  a hanyar Birnin Gwari ko  hanyar Kachiya  a shinfida wannan jami’a a ajiye ta wuri daya, wadda nan da shekara 100 ba za a yi kukan rashin fili, na gina wani abu ba. Kamar yadda aka  gina jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Amma rarraba tsagayoyin jami’a ba shi da wani tasiri.
    GTK; Har’ila yau a ‘yan kwanakin nan gwamnatin ta jihar Kaduna ta sake yunkurowa don rage yawan ma’aikatan kananan hukumomin  jihar mene ne za ka ce kan wannan al’amari?
    Farfesa Dadari; Maganar ma’aikatan kananan hukumomi kamar maganar malaman makarantun firamare ne, a baya an dauki mutane aiki a kananan hukumomi ba kai ba gindi. An dauki mutane ba sa aikin komai a kananan hukumomi an ce su je su ci abinci. Na san mutane da dama wadanda yaransu suna makaranta ne amma sunayensu suna a wasu kananan hukumomi ana biyansu albashi a matsayin ma’aikata.  Don haka yanzu a kananan hukumomi za ka ga babu kowa sai wata ya kare, mutane suje su karbi albashi.  Babu inda ake yin irin wannan sai a Nijeriya, kuma babu yadda za a sami ci gaba a irin wannan tsari. Amma saboda mutane basa son gaskiya, sai tsine wa wannan yunkuri ake yi. Wannan abu da Gwamna El-Rufa’i yake yi yana yi ne domin  ci gaban al’ummar jihar Kaduna. Duk jihohin Nijeriya irin abubuwan da suke faruwa ke nan.
    GTK; Ganin ana ta koke-koke na rashin ayyukan yi, baka ganin irin wadannan abubuwa za su kara kawo rashin aiki a jihar Kaduna?
    Farfesa Dadari; Akwai sana’o’i da dama da mutane za su iya shiga su koya. Ya kamata bayan mun sa yaranmu a makaranta mu rika sanya su a wuraren koyon sana’a. Ga sana’o’i nan daban-daban wadanda za mu iya
    sanya yaranmu su koya. Sannan ga sana’ar noma wadda ta kun shi abubuwa da dama za mu sa yaranmu su koya. Don haka ba dole ne sai mun yi aikin gwamnati ba. Kuma bai kamata don mutum yana aikin gwamnati yaki yin
    wata sana’a ba. Domin yanzu albashi ba zai isa ma’aikaci ba.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here