SANYA MATA CIKIN GWAMNATI YA KAWO CI GABA A JIHAR KANO-HAJIYA ALPHA DAMBATTA.

    0
    690
    JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
    FITACCIYAR \’yar siyasar nan da ke Dambatta Hajiya Alpha  Abdu Usman Dambatta  ta ce Jihar Kano tana samun ci gaba saboda sanya mata masu yawa cikin gwamnati da Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke yi ba tare da nuna bambanci ba.
    Ta yi wannan tsokaci ne a zantawarsu  da wakilinmu, tare da bayyana cewa ko shakka babu Gwamna Ganduje ya ciri tuta bisa la\’akari da yawan matan da ke cikin gwamnatinsa kuma suke ba da gudummawarsu ga ci gaban jihar ba tare da nuna kasala ba.
    Hajiya Alpha Dambatta ta kuma sanar da cewa matan Jihar Kano suna cin ribar dimokuradiyya idan aka dubi irin abubuwan da ake yi masu na bunkasa dogaro da kai da koyon sana\’o\’i  ta kowane fanni wanda a cewar ta hakan abin a yaba ne kwarai da gaske.
    Daga nan sai ta bayyana cewa matan Jihar Kano za su ci gaba da bai wa gwamnati gudummawa bakin gwargwadon iko ta yadda kwalliya za ta ci gaba da biyan kudin sabulu, inda kuma ta yi amfani da wannan dama wajen yin fatan alheri ga daukacin matan da suke rike da mukamai a cikin gwamnati  kuma suke ba da gudummawarsu ga ci gaban jihar cikin nasara.
    A karshe, ta yi albishir cewa dukkanin matan da suke da mukami cikin gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje za su ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen ba da gudummawa domin ganin Jihar Kano tana kara bunkasa a kowane fanni,sannan ta jaddada cewa jam\’iyyar APC za ta ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofinta na alheri ga al\’ummar Nijeriya.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here