Mustapha Imrana Abdullahi
WATA mace mai dauke da juna biyu da ta halarci Wa\’azin da kungiyar Izala ta kasa (JIBWIS) ta gabatar a Jihar Neja ta haifi da namiji a wajen wa\’azin.
Ita dai matar da ta zo wurin wa\’azin tun daga wuri mai nisan kilomita 70 kamar yadda shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya shaida wa manema labarai.
Abdullahi Bala Lau ya ce hakika faruwar wannan al\’amari ya tabbatar da irin yadda karbuwa da kuma samun shaukin addinin Islama ke kara karbuwa a cikin zukatan jama\’a.
\”Wannan mata da ta taho daga wuri mai nisan kilomita saba\’i\’n ba ta taba zaton za ta haihu ba amma sai ga shi cikin hukuncin Allah ta haifi da namiji an kuma yi masa addu\’o\’i tare da fatar Allah ya sa jinjirin ya zama mahaddacin kur\’ani ne\”.
Ya ci gaba da cewa a matsayinsu na shugabannin kungiyar Izala sun ba matar gudunmawar kudi dubu hamsin wadansu mutane kuma sun ba su taimako buhunan shinkafa,masara, gero da sauran taimako iri-iri domin nuna murna da farin ciki, an kuma yi wa matar da mijin ta tare da Muhammadu Buhari shugaban Nijeriya addu\’o\’i sosai.