Rundunar Ba Da Kariya Ta Cafke  Matasa 20

0
812

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR ba da kariya ta kama matasa 20 a jihar Borno da ake  zarginsu da laifuka daban daban da suka hada da karkatar da abincin ‘yan gudun hijira da sace kayan hada ruwan famfo da dabbobi kamar akuya tare da bin matan
aure suna yaudararsu suna kwace masu wayoyin hannu. Wasu matasa da suka kirkiro da sabbin salon yin sata a
jihar Bornon sun shiga hannun Civil Defense. Kawo yanzu matasa 20 ne rundunar ba da kariya ta nuna wa manema labarai a zaman wadanda aka kama da laifuka.
Shugaban rundunar, Ibrahim Abdullahi, shi ya gabatar da mutanen gaban manema labarai a garin Maiduguri. Cikin mutanen har da masu karkatar da  abincin ‘yan gudun hijira.
Akwai wasu da ke sayar da katin jabu a sansanonin ‘yan gudun hijira. Akwai masu satar awakai. Wasunsu kuma suna hada baki da ma’aikatar samar da ruwa ta jihar Borno suna sace kayyayakin samar da ruwan.
A wani sabon salo kuma da matasan suka bullo da shi su kan yi cefane su kai gidan wasu mutane su ce an aikosu ne.
Idan sun ba da cefanen sai su ce maigidan ya gaya masu su karbo wasu kayayyaki. Suna kuma iya kwace wayar
uwargidan su ruga da gudu.
Da bakin su matasan suka amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa. Ibrahim Abdullahi shugaban hukumar ba da kariya ya ce matasan basu kyauta ba saboda ko a kayan abinci matasan sun sace buhuna dari biyu na dawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here