An Kadadamar Da Fara Ba Wa Daliban Sakandare Awaki A Katsina

0
709

Rabo Haladu Daga Kaduna

KWAMISHINIYAR Ilimin ta jihar Katsina Farfesa Halimatu Sa’adiya Idris, ta kaddamar da raba awakan kiwo a
makarantar Sakandaren koyon harshen Larabci ta \’yan mata da ke Dutsin-ma GGASS Dutsin-ma.
Da take kaddamar da awakan ga daliban, kwamishiniyar ta bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina ta zabo
wasu makarantun Sakandare guda 20 a duk fadin makarantun shiyoyin Katsina guda uku.
Ta kuma bayyana cewa wannan shirin zai taimaki dalibai wajen samun sakamako mai kyau wajen cinye darasin koyon kiwon dabbobin gida wato “Animals HouseBoundary” tare kuma da karfafawa dalilan samun sana’ar dogaro da kai ta kiwon awakai musamman ga daliban da suke zaune a karkara.

Daga karshe Kwamishiniyar ta yi godiya ga gwamnan jihar KatsinaAminu Bello Masari bisa kulawar da yake bai wa ma’aikatar Ilimi wajen ba suduk abubuwan da suke bukata domin ciyar da Ilimin jihar gaba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here