Daga Usman Nasidi
A ranar Talatar da ta gabata ne \’yan kasuwar suka rinka zubar da hawaye yayin da suke bayyana irin asarar da suka tafka sakamakon wannan gobara da ta afku da misalin karfe 2:00 na dare a babbar hanyar Roadblock da ke daura da wurin sayar da abinci na Chicken Republic.
\’Yan kasuwa sun zubar da hawaye yayin da gobara ta kama shaguna a birnin Akure
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta afku ne sakamakon wata \’yar matsala ta wutar lantarki, inda mazauna yankin suka yi iyaka bakin kokarin su na kashe wutar bayan ta debi a wani tana aika-aika a shagunan kafin zuwan \’yan kwana-kwana.
Dukiyoyi na tarin miliyoyi sun salwanta a cikin shagunan da wannan gobara ta lashe, inda \’yan kasuwar suka bayyana cewa mafi akasarin hajojin su sababbi ne da suke shirin cin kasuwar bikin kirsimeti da kuma sabuwar shekara.