Jabiru A Hassan, Daga Kano.
GWAMNATIN Jihar Kano ta tallafa wa masu sana\’ar shayi domin su kara bunkasa wannan sana\’a tasu, tare da karfafa masu gwiwar ci gaba da dogaro da kai.
Da yake kaddamar fa shirin bafa tallafin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa rukuni-rukuni na masu sana\’oi ta yadda za a kara bude kofofi na dogaro da kai da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar da ma kasa baki daya.
Sannan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki masu sana\’oi da matukar muhimmanci, don haka ne take kara bullo da hanyoyi masu kyau na tallafa wa al\’umma wanda a cewarsa hakan yana daga cikin manufofin gwamnatin jihar Kano na ingantuwar al\’umma ba tare da nuna gajiyawa ba.
Dokta Ganduje ya kuma nunar da cewa gwamnatinsa tana ci gaba da duba hanyoyi masu kyau na taimaka wa al\’ummar Jihar Kano musamman a wannan lokaci da ake ciki,tare da yin albishir ga daukacin al\’ummar jihar cewa akwai kyawawan tanade-tanade da ake da su na kyautata masu kuma sannu-a-hankali za a fahimci hakan.
Wakilinmu ya yi wani bincke kan wannan tallafi da gwamnati ta yi wa masu shayi, inda kuma ya ruwaito cewa an zakulo wadanda suka amfana da tallafin ne daga mazabu 484 da ke kananan hukumomi 44 da ke jihar, sannan an bai wa kowane mai shayi kayan sana\’a da kudin su ya kai Naira Dubu 40 kowannen su inda jimlar kudin suka haura Naira Miliyan 208.
Haka kuma dukkanin masu shayin da suka zanta da Gaskiya Ta Fi Kwabo sun sanar da cewa tallafin ya zo daidai lokacin da ake bukatar sa domin a cewar su, masu sana\’ar shayi da dama sun sake komawa kan sana\’arsu ta shayi bayan rufe rumfunansu da suka yi saboda karyewar jari.