RUNDUNAR YAN SANDA TA HALAKA WASU MASU GARKUWA DA MUTANE A KADUNA

0
731
Daga Usman Nasidi
RUNDUNAR \’yan sandan Najeriya ta sanar da hallaka wasu da ake zargi sun kashe wani shugaban \’yan kato da gora da ke garin Sabon Gayan, cikin karamar hukumar Chikun.
Mamacin, mai suna Haru Manya ya rasa ransa ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba yayin da yake aiki a gona, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ya ruwaito.
Kakakin \’yan sandan, Jimoh Moshood, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labaru, a garin Gaya, inda ya ce sun kashe mutanen ne yayin musayar wuta da suka yi da \’yan sanda.
Majiyarmu ta samu labarin cewa an kaddamar da farautar mutanen ne bayan umarnin da Sufeton \’yan sanda na kasa ya bayar, na a kamo duk wadanda ke da hannu cikin kisan Haru.
A wani labarin kuma, Rundunar \’yan sanda ta kama wasu masu garkuwa da mutane su 8; Umar Ibrahim, gang leader, Iliya Adamu, Ifeanyi Linus, informant to the gang, Jibril Adamu, Samaila Haruna, Ibrahim Mamman, Ibrahim Idris da Silas Chukwuemeka. Inda ya ce an ceto mutane 3 daga wajensu.
Jimoh ya ce sun kwato motoci guda biyu, kirar Toyota Corolla, kananan bindigu, da bindiga kirar AK47, da alburusai da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here