Suna Shirin Yi Wa Dokar Fyade Da Luwadi Kwaskwarima

0
882
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
MAJALISAR dokokin Jihar Yobe na shirin yin kwaskwarima a dokar shari\’ar nan ta Penal Code da ta tanadi hukunci a kan mutanen da ke aikata laifuffukan nan da suka shafi fyade da kuma luwadi a tsakankanin al\’umma musamman matasa don samun sa\’ida.
Dokar penal code din da bangaren zartaswa ta mika da majalisar dokokin ke mujadala akai ya samu ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisr bayan da mambobin majalisar dokokin su ka yi doguwar muhawara akai.
Da yake jagorantar wannan muhawara shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Usman Adamu ya ce matukar sun kammala muhawara kan wannan doka har ta zama hakika kan iya rage yawaitar aikata wadannan muggan
laifuffuka na fyade da kuma luwadi a tsakankanin matasa.
Alhaji Adamu Usman ya kara da cewar wannan shari\’a ta penal code ta yi tanadin hukunci kan wadannan laifuffuka amma duk da haka hukuncin bai isa ba, don haka ya zama wajibi su kara mata karfi.
Shugaban masu rinjayen ya ce wannan doka da suke kokarin kwaskwarewa za ta tanadi hukuncin daurin shekaru 25 a gidan jarun ba tare da zabin biyan tara ba.
Da suke ba da gudummawarsu dangane da wannan muhawara babban mai tsawatarwa a zauren majalisar Bukar Mustapha da Bulama Bukar da Gafo Mai Zabu Bizi da kuma Ahmed Musa Dumbol sun ce matukar sun tabbatar da
wannan doka to kuwa hakan zai taimaka wa gwamnati wajen raguwar aikata wadannan laifuffuka na fyade da luwadi.
Shugaban wannan majalisa ta dokokin Jihar ta Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo ya yaba wa \’yan majalisar dangane da yadda suka ba da cikakken goyon baya dangane sake kara karfi a wannan doka kan laifukan fyade da luwadu.
Don haka kakakin majalisar ya shawarci iyaye da akullum su rika sa ido ga shige da ficen \’ya\’yansu kana su kokarta ganin cewar duk wanda ya aikata laifuffukan da aka ambata su taimaka don fallasa su tare kuma da mika su ga kotu don hukuntasu.
Alhaji Adamu Dala Dogo ya mika wannan doka ga kwamitin da ya kunshi shari\’a da addini da su yi aiki a kanta na tsawon makonni biyu don sake dawo da ita zauren majalisar don rattaba mata hannun karshe daga nan sai a mika ga bangaren zartaswa don zama doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here