Za Mu Biya Korarrun Malamai Hakkokinsu… Inji Samuel Aruwa

0
974

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Kaduna ta jadda kudirinta na ganin duk malaman makaratun firamare da za ta kora ta biya su hakkokinsu na barin aiki.
Hakazalika, gwamnatin ta bayyana cewa babu siyasa cikin gyaran fasalin harkar ilimi a fadin jihar,hasalima, gyaran zai kawo ci gaban harkar ilimi.
A zantawarsa da wani gidan rediyo, kakakin gwamnan jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta tabbatar da cewa duk wani malami da aka kora daga aiki bisa rashin cin jarabawar kwarewa da aka shirya masa, zai samu hakkinsa na barin aiki, yana mai cewa ” Dole za mu biya su hakkokinsu bayan haka kuma yanzu an kafa wani kwamiti da zai karbi koken malaman da suka fadi jarabawa, sa’annan kuma wannan aiki ba shi da nasaba da siyasa ko kuma niyyar zalunci.
Da yake bayani dangane da daukar Malamai, Aruwan ya ce, duk wadanda za a dauka aikin malunta bayan sun gabatar da takardun karatu, su ma sai an yi musu jarabawa domin gane kaifin basirar su.
Samuel Aruwan, ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ta himmatu wajen kawo gyara a harkar ilimi a jihar baki daya, yana mai cewa, wannan shirin za a ci gaba gudunar da shi.
A zantawarsa da wakilinmu, shugaban hukumar bayar da ilimi na bai-daya, Malam Nasiru Umar, ya bayyana cewa
” babu siyasa a cikin wannan lamari saboda kannena guda uku da matar kanina wadanda muke uwa daya uba daya duk sun fadi jarabawar, kuma ina da damar da zan taimake su amma na ce gyara za mu yi kuma dole ta taba kowa da kowa, wannan shi ne batun gaskiya” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here