AN KAMMALA TARON KUNGIYAR RAJIN  TAIMAKA WA AL\’UMMA TA IACD A KANO

1
809
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AN kammala babban taron kungiyar nan mai rajin taimakawa al\’uma ta kasa da kasa watau \” International Association For Community  Development\” (IACD) wanda aka gudanar a tsangayar kimiyyar kula  da muhalli ta jami\’ar Bayero da ke Kano a ranakun 13 da 14 ga wannan wata na Nuwamba.
Taron wanda ya sami halartar wakilan kungiyar daga jihohin kasarnan 36 har da birnin tarayya Abuja, an yi shi cikin nasara da fahimta musamman ganin yadda mahalarta taron suka nuna gamsuwar su bisa yanayin abubuwan da aka tattauna da irin kasidun da aka gabatar da kuma tambayoyin da masana suka amsa nan take.
Sannan taron ya sami halartar wasu daga cikin kusoshin gwamnatin jihar ta kano wadanda suka gabatar da jawabai tare da jaddada goyon bayan gwamnatin jihar ga wannan kungiya mai mambobi a ko\’ina a duniya wadda kuma ta himmatu wajen jawo al\’umma cikin aiyukan taimakon jama\’a a matsayin taimakon kai.
Tun da fari a jawabin sa ga mahalarta taron, mataimakin shugaban kungiyar na yankin Nahiyar Afirka, Farfesa Muhammad Bello Shitu ya isar da sakon shugaban kungiyar na duniya watau Paul Lachapelle na jami\’ar Montana dake kasar Amurka, inda ya ce yana fatan alheri ga daukacin mahalarta wannan taro kuma yana fata kowa zai kara azama wajen taimaka wa al\’umma kamar yadda manufofin kafa kungiyar suke.
Haka kuma ya sanar da cewa kungiyar ta IACD za ta ci gaba da aikin hada kan al\’umma domin su taimaki juna ta yadda kowa zai sami rayuwa mai amfani da albarka ta kowace  fuska,tare da yaba wa kokarin manyan jami\’an wannan kungiya irin su Farfesa Muhammad Shitu wajen aikin bayyana kyawawan manufofin kungiyar ba tare da nuna kasala ba.
Dukkanin mutanen da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa kungiyar ta IACD tana da manufofi masu kyau, sannan tana da tanade-tanade masu matukar amfani ga al\’ummar duniya idan aka dubi irin kokarin da take yi tun kafuwarta.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here