AN SANYA RANAR ZABEN KANANAN HUKUMOMI A JIHAR KANO

    0
    933
    Jabiru A Hassan, Daga Kano.
    HUKUMAR zabe ta Jihar Kano watau KANSIEC ta sanya ranar 10 ga watan Fabrairun shekara ta 2018 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben kananan hukumomi domin samar da zababbun shugabannin kananan hukumomi a tsari irin na dimokuradiyya.
    Shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai, tare da jaddada cewa hukumarsa za ta yi shiri ingantacce domin tabbatar da cewa an gudanar da zabe mai gamsarwa kamar yadda yake cikin tsare-tsarenta.
    Ya ce kafin lokacin zaben, za a gudanar da wani gangami na wayar da kan al\’umma masu zabe a dukkanin kananan hukumomin da ke fadin jihar, sannan hukumar ta KANSIEC za ta yi dukkan abin da ya kamata wajen ganin an yi wannan zabe cikin nasara da kwanciyar hankali.
    Haka kuma ya bukaci dukkanin masu sha\’awar tsayawa takara a kowane mataki da su bi dukkan ka\’idoji da sharuddan da aka sanya domin cimma nasarar zaben wanda a cewar sa, kowane dan jam\’iyya yana da rawar da zai taka domin ganin an yi zaben cikin jin dadi da farin ciki.
    Wasu \’yan siyasa da wakilinmu ya tattauna da su dangane da sanya ranar zaben sun yaba da yunkurin gwamnatin Jihar Kano na tsayar da ranar zaben kananan hukumomi  a jihar tun bayan karewar wa\’adin wadanda suka gabata,tare da fatan cewa za a yi wa abokan hamayya adalci a zaben.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here