Dara-ta-ci-gida: Wani Dan Sanda Ya Je Sata Ya Baro Katin Shaidarsa

0
688

Rabo Haladu Daga Kaduna

WANI jami’in dan sanda mai suna Williams Godwin ya jefa kansa cikin tsomomuwa bayan da ya baro katin
shaidar sa na aikin dan sanda a cikin jakar wani dan shekara 41 a duniya da ya yi wa fashi da makami.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa dan sandan ya tare mutumin ne a kan hanyarsa ta zuwa Legas daga Ibadan
inda kuma ya sace masa dukkan katunan bankinsa da kuma kudadensa Naira Dubu hudu.
Mun dai samu cewa sai dai a yayin da dan sandan ke bincika jakar mutumin sai katin shaidarsa ya fada ciki shi
kuma bai lura ba.
Da yake karin haske game da lamarin, Godwin ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan da ya
gabata na Oktoba inda kuma ta tabbatar da cewa dan sandan har kusarsa ya yi da wani abu mai tsini a gefen wuyansa.
Tuni dai jami’an ‘yan sandan suka baza komarsu suna neman jami’in da yanzu haka ya bi uwa duniya ya boye.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here